Zangola Makama, gwani wurin labaran hare-hare ya bayyana cewa ‘yan ta’adda wanda ake kyautat zaton ‘yan ISWAP ne sun kashe matafiya shida a Borno.
Wannan lamarin ya faru ne ranar asabar a arewacin jihar ta Borno inda kuma yace sun kona wasu motoci akan hanya bayan sun budewa mutane wuta.
Amma sun tsere yayin da suka hango jami’an tsaro na riskar su.