‘Yan ta’addan siyasa sun tayar da hankulan al’umma sun hanasu yin rigistar katin zabe a Ilesa dake yammacin jihar Osun.
Kuma wani mazaunin yankin ya bayyana cewa ‘yan ta’addan sun kaiwa ofishin sakateriyar PDP hari dake yankin.
Yayin da jami’an tsaro na Civil Defence suka bayyana cewa ‘yan ta’addan sun kai harin ne a karamar hukumar Ilesa dake yammacin Osun a guduma ta 1, 3 da kuma ta 7.