fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Yan wasan Atletico Madrid guda biyu sun kamu da cutar Covid-19

Tawagar kungiyar Atletico Madrid da zasu yi tafiya izuwa garin Libson dake kasar Portugal sun yi gwajin cutar korona kafin su gudanar da atisayi ranar sati, kuma sakamakon gwajin ya fito ranar lahadi yayin daya bayyana cewa mutane biyu sun kamu da cutar kuma gabadayan su yan wasa ne.

Yan wasan guda biyu sun killace kansu bayan an tabbatar da cewa sun kamu da cutar, kuma yanzu kungiyar tana shakkar cewa watakila wani kamu cikin sauran mutane 93 da zasu yi tafiya izuwa garin Libson ranar litinin domin su cigaba da buga sauran wasannin gasar zakarun nahiyar.
Za’a sake yiwa gabadaya tawagar gwajin cutar ranar litinin wanda hakan zai sa su jinkirta tafiyar tasu saboda sai sun jira sakamakon sabon gwajin da suka yi kafin su yanke shawara.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Kungiyar PSG ta kori kocinta Maurizio Pochettino

Leave a Reply

Your email address will not be published.