fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Yan wasan Chelsea guda hudu sun kamu da cutar Covid-19, kuma wasu guda hudu suna killace kansu

A takaice yan wasan Chelsea guda takwas suna killace kansu bisa sharruddan da gwamnatin ta tasara na cutar korona, kuma Goal sun tabbatar da cewa yan wasa guda hudu ne sun kamu da cutar ta a cikibn su. Goal sun kara da cewa Mason Mount,Tammy Abraham,Christian Pulisic da Fikayo suna cikin yan wasan amma sai dai ba’a da tabbacin cewa suna cikin wa’yanda suka kamu.

Har yanzu dai ana sa ran cewa Mason Mount da Tammy Abraham zasu bugawa kasar Ingila wasa bayan an saka sunayen su a cikun tawagar Gareth Southgate da zasu buga gasar kofin kasashe mai zuwa a watan satumba. Chelsea sun gudanar da gwajin cutar korona a karshe makon daya gabata saboda zasu dawo atisayi kafin a fara buga kaka mai zuwa nan da 12 ga watan satumba.
Watakila wasu daga cikin yan wasan guda 8 suna bin dokar da gwamnati ta tsara ne akan matafiya, yayain da kasar UK ta tilasta dokar killace kai na tsawon kwanaki 14 ga dukkan mutanen da suke shigowa daga kasashen cutar korona tayi kamari. Shirin da frank Lampard yake yi na fara sabon kaka yaja baya saboda yan wasan shi guda takwas suna killace kansu.
Chelsea ba itace kadai kungiyar Premier League data kamu da cutar korona ba, yayin da itama kungiyar Sheffield United, West Ham da kuma Brighton duk suka kamu da wannan cutar a cikin tawagar su.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.