fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Yan wasan Manchester United guda biyu sun wallafa sakon bankwana a shafukan suna yanar gizo bayan sun bar kungiyar

United sun sanar a kwanakin baya cewa wasu yan wasan su zasu bar kungiyar a karshen watan yuni, kuma biyu daga cikin tawagar yan wasan da suka bar United a jiya sun wallafa wani rubutun bankwana mai taba zuciya ga kungiyar da suka kasance suna so tun yarintar su.

Cameroun Borthwick Jackson da Dametri Mitchell suna cikin yan wasa goma da suka bar United a jiya bayan kungiyar taki yi masu sabon kwantiraki. Angel Gomez shima yana cikin yan wasan da suka bar kungiyar da Dion McGee, Ethan Hamilton, George Tanner, Aidan Barlow, Kien O’Hara, Alex Fojticek da Largie Ramazani.

Borthick mai shekaru 22 ya buga wasanni 14 a  tawagar yan wasan 11 na farko a united karkashin jagorancin Louis Van Gaal shekara ta 2015/16, kuma ya kasance a kungiyar tun yana dan shekara 5. Dan wasan ya wallafa a shafin shi na Instagram cewa bayan shekaru 17 a United gashi zai bar ta a rana guda, bayan ya taso a kungiyar kuma bai da wani burin daya wuce yin wasa a United.

Karanta wannan  'Yan wasan Manchester sun bukaci a sayar da Ronaldo kuma har yanzu baya jituwa da sabon kocin kungiyar

Mitchell wanda wasa daya kacal ya buga a tawagar yan wasan 11 na farko ya saka wasu hotunan shi na lokacin da yake kungiyar,kuma yayi wani rubutu cewa ya gode wa ahalin Manchester United. Dan wasan ya kara da cewa tun yan dan shekara shida babu wani abun daya sani illa kungiyar United.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.