fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

‘Yan wasan Tamola a jihar kogi sun yi Zanga-zangar kin biyan su Alawus na tsawan shekara 2

‘Yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Kogi United a ranar Alhamis din da ta gabata sun gudanar da wata zanga-zangar lumana a gidan gwamnatin jihar don nuna rashin jin dadin su na rashin biyan su alawus-alawus dinsu na tsawan shekaru biyu.

‘Yan wasaan wadanda ke sanye da kayan kwallo sun yi tattaki zuwa gidan gwamnatin jihar don mika korafinsu ga Gwamna Yahaya Adoza Bello.
Inda Su katoshe kofar gidan Gwamnatin jihar tare da yin barazanar ci gaba da zanga-zangar har sai an biya musu dukkan hakkokinsu.

Haka zalika fusatattun ‘yan wasan sun kuma yi barazanar kauracewa wasu wasannin muddin a cewarsu aka kasa biyan bukatun su.

Haka kuma ‘yan wasan sun yi ikrarin cewa karin Al’bashin da gwamnatin jihar tai musu Sam basu gani a kasa ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.