An kama me gadin Makabartar Surulere dake jihar Ondo tare da wasu mutane suna tono kaburbura suna cire sassan jikin mutane.
Lamarin ya faru a jiya, Lahadi, 17 ga wata Janairu inda kuma nan take aka kira ‘yansanda suka yi awon gaba dasu.
Saya daga cikin shaidun gani da ido ya bayyana cewa ganim wani mutum na ta zarya a kofar makabartar tasa suka ce bari su ga abinda ke faruwa inda kuma suka kamasu.