fbpx
Monday, December 5
Shadow

Yanda farar hula, Hussaini Mafa, ya ceci wasu sojoji daga hannun ‘yan Boko Haram

Wannan wani bawan Allhane me suna Hussaini Mafa wanda rahotanni suka bayyana cewa ya ceci sojoji kusan biyar daga hannun mayakan kungiyar Boko Haram a lokacin da suka kai hari garin Baga na jihar Borno.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Hussaini ya kasance babban manomin Albasa kamin zuwan mayakan Boko Haram garin nasu, amma yanzu ya gudu da iyalanshi inda ya koma aikin lebura a wani gurin gini dan ya samu abinda zaici da Iyalanshi.

Da yake bayar da labarin abinda ya faru, a lokacin da boko haram din suka kawo hari garin nasu na Baga kuma suka ci karfin sojoji, wasu sojoji sun shigo gidanshiinda suka nemi mafaka, haka ya basu kayanshi suka saka, suka binne kayansu na sojojin a cikin kasa, suka dunguma shida iyalanshi da sojojin suka kama hanyar tafiya Maiduguri a kafa.
Ya kara da cewa abinda ya gani ya matukar tada mishi da hankali, sojoji sun ajiye makamai suna rokon ‘yan Boko Haram din afuwa amma sai yankasu sukeyi, ya kuma fada cewa, tafiyar da yayi da sojojin ba karamin saka kanshi da iyalanshi yayi cikin hadari ba, dan da ‘yan Boko Haram din sun ganosu baisan abinda zasu yi musuba.
Allah shoi kyauta, ya kuma kawo mana zaman kafiya a kasarmu. 


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Karanta wannan  An kashe ƙasurguman ƴan fashin daji da ke addabar jihar Zamfara

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *