fbpx
Saturday, May 21
Shadow

Yanda farashin man fetur ya karu daga N87 zuwa N165.77 tun bayan da shugaba Buhari ya karbi mulki zuwa yanzu

Daga watan Disamba na shekarar 2015 zuwa watan Disamba na shekarar 2021, farashin man fetur ya karu daga Naira 87 akan kowace lita zuwa Naira 165.77.

 

Hakan na nufin an samu karin kaso 90.54 cikin 100 na farashin a tsakanin wadannan shekaru.

An samu wadannan bayanai ne daga kundin ajiyar bayanai na babban bankin Najeriya, CBN, kamar yanda Punchng ta ruwaito.

 

Hakaman kuma shima farashin dala ya karu daga 197 da ake sayenta a baya zuwa kusan har Naira 500 a shekarar 2016.

Wani abu dake kara ciwa ‘yan Najeriya tuwo a kwarya shine maganar tallafin man fetur dake lakume biliyoyin kudade duk shekara.

Karanta wannan  Mulkin Nijeriya Na Bukatar Shugaba Mai Dan Tabin Hankali>>Obasanjo

 

Gwamnatin tarayya na maganar cewa talaka bai amfana da wannan tallafin man fetur din inda taso cirewa, amma daga baya ta fasa.

 

Kamfanin mai na kasa, NNPC, ya bayyana cewa, Tallafin man fetur din ya lakume biliyan 306.92 a shekarar 2015, yayin a kuma ya lakume tiriliyan 1.43 a shekarar 2021.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.