PRNigeria ta ruwaito cewa gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya baiwa kamfanin Boge da babushi a zahiri kwagilar gina titi me tsawon Kilometres 1 akan Naira Miliyan 110.
Gwamnan Ganduje ya baiwa kamfani me sunan Stonegate Quaries Limited aikin ne a shekarar 2019 wanda yanzu a watsar da aikin.
Kuma bincike da aka yi kan inda kudin aikin suka shiga ya ci tura, dan jami’an gwamnatin jihar sun kasa amsa tambaya kan ina kudin suke.
Rahoton yace, titin da ake magana akansa shine Ado Bayero Road dake Dorayi Babba a karamar hukumar Gwale.
A shekarar 2019 an fitar da Naira Miliyan 38 dan fara aikin titin inda a shekarun 2020 da 2021 aka fitar da sauran kudin a kasafin kudin jihar, kamar yanda majiyar ta ruwaito.
Saidai duk da haka babu wani alamar aikin gyaran titin kokuma alamar cewa ana kan aikinsa.
A takaice dai, kamfanin ma da aka ce an baiwa aikin gyaran titin babushi a zahiri. Majiyar, taje hukumar CAC dakewa kamfanonin Najeriya rijista inda ta binciki cewa ko kamfanin da aka baiwa kwangilar na da Rijista? Hukumar tace a’a.
Hakanan kokarin gado Adireshin kamfanin da akece yana Abuja shima ya faskara.