Kwamishiniyar kula da walwala ta jihar Kaduna, Hafsat Baba ta bayar da labarin yanda iyaye ke bada ‘ya’yansu mata wajan ‘yan Bindiga ana lalata dasu ana basu kudi.
Ta bayyana hakane a Abuja wajan taro kan mata ranar Laraba.
Tace matan dake bayar da ‘ya’yansu a matsayin masu aikin gida suna taimakawa yawan yaran da ake samu wanda basa zuwa makaranta.
Ta bayar da misalin alkaluman UNICEF wanda suka nuna yara mata miliyan 10 ne basa zuwa makaranta a Najeriya.
Tace irin yaran da ake dorawa talla zaka gansu akan tituna, abin bakin ciki shine, wani lokacin ma sune ke ciyar da mutanen gidansu.
Ta kara da cewa ta ma samu labarain ana bayar da ‘yan mata wajan ‘yan Bindiga suna lalata dasu su baiwa iyayen yaran kudi.