fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Yanda Kungiyar IPOB ta shiga Dimuwa bayan kama Nnamdi Kanu

Kama mai fafutukar ɓallewa daga Najeriya Nnamdi Kanu ya jefa ƙungiyarsa cikin ruɗani wanda ka iya kawo ƙarshenta gaba ɗaya.

Shugaban ƙungiyar ta IPOB da ke kudancin Najeriya na son ɓallewa a yankin kudu maso gabashin Najeriya don kafa ƙasa ta daban.

Kuma Kanu ya samu goyon bayan dubban mazauna yankin da ke yi masa kallon gwarzo kuma mai kishin yankinnasu.

Sama da shekaru 10 yana kumfan baki a gidajen rediyo da kafafen sada zumunta yayin da gwamnatin Najeriya ta riƙa ɗaga masa kafa.

Sai a shekarar 2020 a lokacin da fafutukarsa ta rikiɗe, bayan da magoya bayansa suka ɗauki makamai ne hukumomi suka fara tunanin taka masa birki.

Ana zargin ɓangaren IPOB da ke ɗauke da makamai da ake kira Eastern Security Network da kisan aƙalla mutun 60 mafi yawancinsu ƴan sanda. Amma sun musanta zargin.

Kama Mista Kanu da aka yi ranar Lahadi kan iya zama wani yunƙuri da zai kwantar da fafutukar.

Hotunan kama shi babu shakka za su kashe ƙwarin gwuiwar mabiyansa.

Dama ana zargin Kanu da kankane shugabancin IPOB ba tare da kafa wasu jiga-jigai da za su iya jagorantar ƙungiyar ba a gaba, hakan tasa a yanzu babu wani ƙwaƙƙwaran shugabanci a IPOB.

”Rikici kan kuɗi da rashin tuntuɓar masu ruwa da tsaki kan abin da ya shafi kafa ɓangaren da ke ɗauke da makamai bai yi wa wasu daɗi ba, a cewar wakiliyar sashen Igbo na BBC Chiagozie Nwonwu, wanda ya yi hira da Nnamdi Kanu a shekarar 2019 lokacin da ya ke gudun hijira.

Wani wanda ya tsere tare da Kanu bara shi ne mataimakinsa Uche Mefor, wanda shi ya riƙe ƙungiyar a karon farko da aka kama mai gidansu.

Kazalika zargin karkatar da kuɗaɗen tallafi da aka samu ya sa wasu magoya bayan IPOB da ke zaune ƙasashen Amurka da Burtaniya ficewa daga ƙungiyar.

Haka ma IPOB ta samu naƙasu sosai a cikin gida, bayan da jami’an tsaro suka fara yaƙi da su.

An kashe masu gwammai a ƙungiyar tare da tsare wasu a gidajen yari.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.