fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Yanda Layar Zanar wani dan Damfara ta ki aiki yayin da ‘yansansa suka je kamashi

Dubun wasu ‘yan damfara ya cika a jihar Legas yayin da wata mata da suka dauka a Mota ta kwarma musu Ihu har ‘yansanda suka kamasu.

 

Matar tace ta shiga Motarsu amma sai ta ga alamar ‘yan Damfarane kuma sun canja hanyar da ba inda ya kamata su kaita ba.

Tace sunzo daidai wani banki sai taga ‘yansanda ta kurma Ihu ananne aka kamsu.

 

Wata mata ma data bayyana cewa sun kwace mata Dubu 150 tace ta hau motane suka bata wani abu tasha, hankalinta ya gushe suka kwace mata Dubu 150.

Karanta wannan  Kungiyar magoya bayan Tinubu ta bayar da shawarar ya dauki Gwamna Elrufai a matsayin mataimakinsa

 

Bayan kamen Nasu, sun tona Asirin wanda suke aikin tare inda ‘yansanda suka je kamasu. A nanne wani daga cikinsu yaso bacewa ta hanyar amfani da wani sihiri yana sambatu amma qbin yaki.

 

Hukumar ‘yansanda dai tace ta kwato motoci da kudi da sauran kayayyaki a hannun masu laifin inda tasha Alwashin gurfanar dasu gaban Kotu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.