fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Yanda Likitoci da malam jinya suka yi ta kansu bayan da aka kai marasa lafiyar da ake tunanin suna da Coronavirus/COVID-19 a Asibitin Legas

Wani lamari daya faru a Asibitin Gwamnati na Gbagada dake jihar Legas kan marasa lafiya na Coronavirus/COVID-19 da aka kai ya dauki hankula.

 

Wasu farar fatane tan kasar Misra/Egypt aka kai asibitin su 4 suna fama da rashin lafiya tsakar dare.

 

Daya daga cikinsu yana ta tari ba kakkautawa, kamar yanda wata majiyar Asibitin ta shaidawa jaridar Punch.

 

An kaisu Asibitinne a motar gida, koda likitoci da masu jiyya suka yi arba dasu, suka ga kuma fararen fata ne sai kowa yayi ta kansa suna fadin,”Coronavirus/COVID-19 ba da mu ba”

 

Likitocin sun kirawo masu gadin Asibitin nesa nesa suna gaya musu cewa a fitar da marasa lafiyar daga Asibitin dan nan ba gurin duba masu Coronavirus/COVID-19 bane.

Karanta wannan  Hotuna: Kungiyar kiwon lafiya ta kaiwa shugaba Buhari ziyara a fadarsa

 

Nan suma dai masu gadin suka yi ta masa suka fitar da marasa lafiyar.

 

Shugaban Asibitin, Dr. Adeleke Kaka ya bayyanawa Punch cewa lamarin ya faru da gaske amma mutum daya ne aka kawo daga wani asibiti me zaman kasa.

 

Kuma da suka ga yanayinshi shine sukace a kaishi babban asibiti. Ya karyata cewa likitoci da malam jinya sun yi ta guje-guje saboda ganin marasa lafiyar.

 

Rahoton yace mutane da yawa sun dauke marasa lafiyarsu daga Asibitin bayan faruwar lamarin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.