fbpx
Sunday, February 28
Shadow

Yanda Magidanci ya bankawa gidansa wuta ya kone Kurmus dan kada ya barwa ‘ya’yansa gado a Kaduna

Wani magidanci, Musa Aga dake unguwar Gwanin Gora ta jihar Kaduna ya babbake gidansa da kansa.

 

Magidancin yayi hakand bayan da ‘ya’yanshi suka tursasa masa cewa sai ya zauna da mahaifiyar su da suka rabu kusan shekaru 20 da suka gabata.

 

Musa ya bayyana cewa yacewa ‘ya’yan nashi ba zai zauna da magaifiyarsu ba amma suka takurashi, suka je ta saman gida ma suka saka kayan Mahaifiyar tasu.

 

Da aka tambayeshi shin baya tunanin barwa ‘ya’yan nasa wani abun Gado ganin cewa ya tsufa, sai yace ai ‘ya’yan arziki ake barwa gadon Dukiya, ‘ya’yansa kuwa ba na gari bane tunda basa son abinda yake so. Yace sun ce masa ai gidan Ubansu ne kuma dole mahaifiyarsu ta zauna a gidan ubansu, yace to yanzu gashinan babu gidan.

 

Mutumin wanda tsohon ma’aikacin gwamnatin jihar Kadunan ne ya bayyana cewa da Kudin kammala aikinsa ya gina gidan amma bacin rai yasa ya konashi.

 

An dai taru makwabta dan kashe wutar amma ta gagara saboda yanayin sanyi, daya daga cikin ‘ya’yan Musa tace takardun Makarantarta take tunani.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *