fbpx
Sunday, December 4
Shadow

Yanda masu zaman gidan kaso a kasar Isra’ila ke dabarar samun haihuwa da matansu ta barauniyar hanya

A kasar Isra’ila akwai falasdinawa wanda aka yankewa hukuncin zama gidan kaso na tsawon shekaru saboda laifika daban-daban da suka aikata, masu iyali daga cikinsu na yin dabarar fitar da maniyyinsu ta barauniyar hanya dan kaiwa matansu dake can gida, a saka musu a mahaifarsu dan su samu su haihu.

Kamar yanda wani me suna mustafa dake zaman gidan kaso yake gayawa wakilin Aljazeera a wata hira da yayi dashi.

Ya kara da cewa wannan itace hanya daya tilo da zasu iya kasancewa da matansu ba tare da matan nasu sun manta dasu ba sun samu wasu mazajen sunyi aureba.

Shi Mustafa yana da da namiji da matarshi me suna Maya ta haifa mishi ta irin wannan hanyar ta fitar da maniyyinshi ta barauniyar hanya, kuma an sakawa dan nashi suna Assad.

Matar wani shima dake zaman gidan kason a kasar Isra’ila ta shaidawa wakilin Aljazeeran cewa mijinta ya fito da maniyyinshi ta barauniyar hanya kusan sau goma kenan, aka saka mata a mahaifarta amma har yanzu Allah be sa ta dauki ciki ba, yanzu dai ta mika lamarinta ga Allah, kamar yanda tace.

Karanta wannan  Shaykh mufti Ismail Menk taréda Farfesa Isa Alí Ibrahim (Pantami) a wajén taron zaman lafìya da hadin kai na dunìya 2022 da ké gudana yanzu haka a bírnín tarayya Abuja

To  saidai hukumomin kasar Isra’ila sun gano wannan abu da fursunoni keyi inda suka sanya tsattsauran mataki akan yanda masu ziyara zasu rika zuwa ganin ‘yan uwansu .

Haka kuma duk yaron da aka haifa  ta irin wannan hanyar ba za’a bashi takardun shaidar zama dan kasa ba ko kuma wata takardar shaidar da zata bashi damar yin tafiya zuwa wani guri ba, haka kuma bazai iya ziyartar mahaifinshi dake gidan wakafiba, domin jami’an kasar suna mai kallon cewa ba dan halak bane.

Assad dan Mustafa da aka haifa ta wannan hanyar shima ya fuskanci irin wannan cikas, an hanashi ganin mahaifinshi, saidai mahaifiyarshi tace duk da haka tana farinciki da samunshi domin zai zamar mata abin alfahari

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *