fbpx
Monday, August 8
Shadow

Yanda mutanen Kauyen Jange dake jihar Zamfara suka kasa zama a garinsu saboda gaza biyan diyyar da ‘yan Bindiga suka dora musu

Hari na farko da ‘yan Bindiga suka kai kauyen ya farune ranar 31 ga watan Yuli kamar yanda wani daya fito daga kauyen kuma a yanzu yake gudun hira ya fada, yace baya so a bayyana sunansa saboda gudun kada ‘yan Bindigar su kai masa hari.

 

Yace ‘yan Bindigar sun sace mutane 6, Maza 5 mace 1, itama saboda Mijinta ba ya nan shiyasa aka tafi da ita. Ya ci gaba da gayawa Sahara Reporters cewa sun nemi a biya Miliyoyin Naira a matsayin kudin fansa amma kamin a biya kudin sai wanda suka sace din suka tsere.

Yace kamin wanda suka tsere din su kai gida sai ‘yan Bindigar suka kira sukace a kai kudin da aka tara koda basu cika ba, da wanda suka je kai musu kudin suka hadu dasu sai suma suka yi garkuwa dasu.

Karanta wannan  Shugaba Buhari yace a lahire ne kadai babu matsar tsaro

 

Yace amma suma daga baya sun kubuta. Dalilin hakane yasa ‘yan Bindigar sukawa gaba dayan kauyen dake karamar hukumar Gusau barazanar cewa zasu tasheshi idan mutanen kauyen basu biya kudin fansar.a

 

Yace tun daga wannan barazanane sai mutanen kauyen suka fara neman tsira suna guduwa dan kada ‘yan bindigar su kashesu. Yace babu sauran yan sa kai saboda duk sun mika makamansu da sunan an yi sulhu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.