Wani Magidanci, Amzat Ibrahim ya bayyanawa kotun Ile-Tuntun dakw Ibadan cewa matarsa mazinaciyace tana cin amarsa.
Hakan ya biyo bayan neman da matar tayi da a raba aurensu. Yace ta gudu wajan watanni 3 inda ta tafi tare da ‘ya’yansa.
Yace abin mamaki sai gashi ya kamata da abokinsa a gado tana cin amarsa.
Saidai Zainab ta bayyana cewa mijinta na yawan cin zarafinta ga zagi a bainar jama’a. Tace kuma hakanan sai yayi ta bibiyarta duk inda zata yanawa rayuwarta barazana.
Alkalin Kotun, Henry Agbaje ya nemi duka 2n su kawo shaidu kan ikirarin da suka yi sannan kuma su zo da wakilansu inda ya daga karar zuwa 2 ga watan Nuwamba.
“My lord, the truth is that Zainab and I fight because of her infidelity. Zainab and my close friend are romantically involved.
”She disappeared from my house for three months. She took my children away. I later found out that she took them to friend’s house.
“I caught the two of them in bed,” Amzat said.