fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Yanda Oby Ezekwesili ta ki amincewa ta zama mataimakiyar Shugaba Buhari>>Fasto Tunde Bakare

Fasto Tunde Bakare wands yawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari mataimaki a takarar da yayi a zaben 2011 ya bayyana yanda Oby Ezekwesili ta ki amincewa ta zama mataimakiyar shugaban kasar a wancan lokacin.

 

Yace shugaba Buhari ya kirashi ya nemi ya samo masa abokin takara daga kudu wanda zai zama sananne kuma me karfin fada aji tunda kasancewar kasar nada bangare-bangare, ba zai yiyu mutum daya bangare daya ya ci zabe ba.

 

Fasto Bakare a hirar da yayi da Sunnews ya bayyana cewa, ya tuntubi mutane irin su, Farfesa Yemi Osinbajo, Mataimakin shugaban kasa na yanzu da Jimi Agbaje, Ministan Kasuwanci na yanzu, da Niyi Adebayo, yace fasto Enoch Adeboye ne ya hadashi da Ezekwesili amma ta ki amincewa da tayin.

 

Yace fasto Enoch ya bayyana cewa tana da damar kin amincewa da wannan tayi saboda a wancan lokacin yana aiki da bankin Duniya ne kuma ba zata so ajiya aikinta ta kama abinda ba tabbas ba. Yace a karshe dai shugaba Buhari ya sake kiransa yace yanaso shi ya tsaya a matsayin abokin takararsa.

Karanta wannan  2023: Masu cewa a zabi musulmi shugaban kasa, mataimakinsa ma musulmi basu wa Najariya fatan Alheri>>Inji sheikh Halliru Maraya

 

Yace Fasto Enoch Adeboye ne ya karfafa masa gwiwa ya amince da tayin, duk da cewa basu yi nasara ba a wancan lokacin.

The cleric said the current vice President, Prof Yemi Osinbajo, Oby Ezekwesili, Jimi Agbaje, current Minister of Trade and Industry, Niyi Adebayo, were among those he contacted to run with Buhari then.

He said that while Agbeje was dropped along the line, Ezekwesili, who Pastor Enoch Adeboye of the Redeemed Christian Church of God, RCCG, helped him (Bakare) contact, refused to run with Buhari.

“But Pastor Adeboye told me he (Buhari) would need a strong Christian to be his running mate. I said to him that Oby is strong too; he said no, that she must not leave certainty for uncertainty because she was working at the World Bank then,” Pastor Bakare said as quoted by the Sun.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.