Real Madrid ta lallasa Barcelona da kwallaye 2-0, yayin fafatawar El Clasico da suka yi jiya lahadi a gasar La Liga ta Spain.
‘Yan wasan Real Madrid masu masaukin baki Vinicius Junior da Mariano Diaz ne suka ci kwallayen, yayin wasan da fafata a filin wasa na Santiago Bernabeu.
Nasarar dai ta karawa kungiyar ta Madrid kwarin gwiwar burin lashe kofin gasar La Liga na bana duk da cewa yayi wuri a yi hasashen zakarar gasar ta bana. Zalika doke Barcelonan, ya ragewa kungiyar ta Real Madrid radadin kayen da ta sha a hannun Manchester City, yayin fafatawarsu a gasar cin kofin Zakarun Nahiyar Turai.
Yanzu haka dai Real Madrid ke jan ragamar gasar La Liga damaki 56, yayinda Barcelona ke niye damaki 55, sai Kuma Sevilla a matsayi na 3 damaki 46.
Bincike ya nuna cewar akalla mutane miliyan 80 kan kalli irin wannan karawar kai tsaye lokacin da ake yin ta a kasashen duniya.
Tarihi ya nuna cewar sau 180 aka fafata tsakanin Barceloana da Real Madrid a gasar La Liga, inda Madrid ta samu nasara sau 72 Barcelona ma sau 72, suka kuma yi kunnen kunnen doki 36.
A jimlace kuma Real Madrid da Barcelona sun hadu sau 243, Madrid ta samu nasara sau 95, Barcelona kuma sau 96, yayainda kuma suka tashi kunnen doki sau 52.