fbpx
Monday, March 1
Shadow

Yanda Shugaban ‘yansandan Najeriya, IGP Adamu ya bada Biliyan 2 dan a kara masa wa’adin shekara 1 amma bai samu ba>>SR

Sahara Reporters ta yi zargin cewa shugaban ‘Yansandan Najeriya,  IGP Muhammad Adamu ya biya kudi har Naira Biliyan 2 dan a tsawaita masa wa’adin shekara 1 akan mukamin nasa amma kuma bai yi nasara ba.

 

Majiyar tace IGP Adamu ya bibiyi masu fada aji daga cikin sarakuna sannan kuma ya baiwa na kusa da shugaban kasa, Muhammadu Buhari kudaden toshiya har Naira Biliyan 2 dan neman a kara masa wa’adin shekara 1.

 

Saidai daga baya bai samu hakan ba, sai wa’adin watanni 3 aka bashi, wanda sam bai ji dadin hakan ba kamar yanda majiyar ta bayyana. Hutudole ya fahimta daga Rahoton cewa, Shugaban ‘Yansandan bai yi murnar karin wa’adin watanni 3 din da aka masa ba, inda ma ya kulle ofishinsa ya ki karbar masu niyyar tayashi murna.

 

Majiyar tace har malamai IGP ya kawo daga Maiduguri amma duk hakarsa bata cimma ruwa ba. Zuwa lokacin hada wannan rahoto dai, IGP Adamu bai ce komai game da wannan batu ba.

 

“After spending over N2 billion to get one-year tenure (extension), he is very upset and has refused to celebrate his tenure extension. He had brought in marabouts (a Muslim holy man or hermit) from Maiduguri well guarded by MOPOL (mobile police) but their predictions didn’t work.

“He reportedly visited traditional rulers and persons of influence across Nigeria and spent on villa influencers only to get 3 months and he is very sad about it. When the announcement was made, he locked his door; he did not allow senior officers to congratulate him.”

 

“Now, he has embarked on a vendetta mission against those suspected to have campaigned against him in the upper echelon of the police,” the source said.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *