Friday, May 29
Shadow

Yanda Soja da dansanda suka dambace kan karya dokar Tuki

Rahotanni daga jihar Ebonyi sun bayyana cewa wasu an samu Hatsaniya da dambacewa tsakanin wani soja da dansanda saboda karya dokar tuki.

 

Dan sanda me bada hannu ya tsayar da wani Adaidaita Sahu, Keke Napep da ya karya dokar tuki inda me tukin yayi iya kokarinsa wajan ganin an barshi ya wuce amma bai yi nasara ba.

Da yaga ba za’a barshi ba sai ya kira me Keke Napep din wanda soja ne, shi kuma ya na zuwa sai ya nemi wanda ya tsare keke Napep din, nan dai aka samu rashin jituwa har aka dambace, sojan ya kira sauran ‘yan uwansa Sojoji inda suma kuma suka kira karin sojoji daga bariki.

 

Suma ‘yansandan sun hadu inda Sojoji suka rika gyara Bindiga zasu yi harbi, saida manyan Jami’an ‘yansanda suka zo wajan sannan aka samu daidaito.

 

Me magana da yawun ‘yansandan jihar Loveth Odah ta tabbatar da lamarin inda tace fadan cikin gidane da ya kamata ace an warwareshi ba tare da tashin hankali ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *