fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Yanda Tsoho dan shekaru 71 ya min fyade sau 10 ya kuma bani layar bata in rika sato mai masara a Gombe>>Inji yarinya ‘yar shekaru 13

Wata yarinya me kimanin shekaru 13 ta bayyana yanda wani tsoho me kimanin shekaru 71 ya mata fyade har sau goma a jihar Gombe.

 

Yarinyar ta bayyana cewa lamarin ya farune lokacin tana zaune da kakarta. Tace tsohon ya rika bata kayan abinci masu tsada.

Tace ta sanshi kusan tun shekaru 2 da suka gabata.

 

Tace ya rika mata fyade lokuta da yawa amma zata iya tuna cewa ya mata sau 10.

 

Ta kara da cewa ya bata laya wadda ya gaya mata cewa layar bata ce wadda zata rika amfani da ita tana satomai kayan abinci.

Karanta wannan  'Yan ta'addan ISWAP sun dauke manoma shida a jihar Borno

 

Yarinyar ta gayawa Punch cewa tana karatu kuma zata so zama ‘yarsanda nan gaba dan ta taimaka wajan hana miyagun laifuka.

 

Ta kuma kara da cewa, tana so a hukunta tsohon.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.