fbpx
Monday, March 1
Shadow

Yanda wani bawan Allah da aka yi Garkuwa dashi ya lakadawa wadanda suka sace shi dukan kawo wuka ya tsere

Wani bawan Allah dan Najeriya dake zaune a kasar Amurka amma yazo ganin gida kuma aka yi garkuwa dashi, ya samu tsira.

 

Saidai kamin ya tsere daga wajan wandada suka yi garkuwa dashi din sai da ya lakadawa daya dag ciki dukan tsiya.

 

Mutumin me suna Chinwezu an saceshi ne tare da wata mata a ranar 3 ga watan Fabrairu inda aka tafi wani daji dasu Jaridar Eonsintelligence ta ruwaito cewa lamarin ya faru a jihar Abia.

 

Koda suka shiga daji, sai aka barshi da daya daga cikin ‘yan bindigar inda shi kuma a nan karfin zuciya ya zo masa yafara kici-kici dashi har Allah ya taimake shi ya kwace Bindigar dake hannunsa ya kwakkwada masa akai sannan ya tsere.

 

Kakakin ‘yansandan jihar, Dsp Geoffrey Ogbonna ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace an kama daya daga cikin masu garkuwa da mutanen wanda bafulatanine yayin da suka kai wanda ya ji raunin Asibiti.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *