An kama wani tsohon sojan kasar Amurka aka kuma gabatar dashi gaban kuliya, manta sabo dan yimai hukunci akan irin azabtarwar da yake yiwa sabbin sojoji musulmai da ake horar dasu dan zama gwanaye, shidai wannan soja dan shekaru 34 shaidun gani da ido sun tabbar da cewa yana ware sojoji musulmai lokacin da yake bayar da horaswa sannan ya rika kiransu da sunan ‘yan ta’adda, ‘yan kungiyar ISIS.
Sannan kuma ya umarcesu shiga wani injin wanki ya kuma kunna injin wankin dan azabtarwa kawai dan suna musulmai.
Saidai lauyan sojan da ake kara ya ya musanta wannan zargi inda yace tsohon sojan besan cewa sojojin da yake horaswa musulmai bane, kuma yana basu horaswa irin wadda ake baiwa kowane soja.
Amma kotu tayi bincike kuma ta tabbatar da wannan laifi na wannan soja me suna Felix sannan ta tankada keyarshi zuwa gidan wakafi.