fbpx
Friday, July 1
Shadow

Yanda Wani Sabon rikici yaso ballewa tsakanin Hausawa da Yarbawa a Ibadan

An sake samun yunkurin Barkewar wani rikici tsakanin Hausawa da Yarbawa a wani yanki na Jihar Oyo.

 

Lamarin ya farune a wani yanki da ake kira Akpata. Saidai jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yansandan jihar, Olugbenga Fadeyi ya bayyana cewa, an shawo kan Lamarin.

 

Wasu da suka shaida Lamarin kuma BBChausa ta Zanta dasu sun bayyana cewa, an yi harbi amma babu wanda ya Mutu.

 

Mutum na farko ya bayyana cewa, suna cikin masallaci sai suka ji ana guje-guje, wasu a kafa, wasu akan babura.

 

Yace koda suka tambaya sai aka ce musu rikici ne ya barke. Yace amma shi bai gudu ba saboda shi Bakone idan ma ya gudu, Daji ne zai shiga.

Karanta wannan  2023: Karanta Jihohin da masana sukace Atiku da Tinubu zasu lashe zabe a cikinsu

 

Yace ya ji harbin bindiga amma maganar gaskiya shine bai san abinda ya faru ba amma ance an harbi wanine. Ya kuma kara da cewa, lamarin ya farune bayan da wani dan acaba, Bahaushe ya kade wani bayerabe ba tare da ya sani ba. Shine wasu matasan yarbawa suka biyoshi cikin unguwar Hausawa suna duka, Shine Suma Hausawan suka shigar masa.

 

Wani shima da ya shaida lamarin ya ce an harbi mutane 3 amma babu Rahoton mutuwa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.