Wannan hoton wani matashine daya takarkare ya dauki hoto da akuya, hoton ya dauki hankulan mutane sosai a dandalin sada zumunta da muhawara, inda aka rika fadin a yayinda wasu ke daukar hoto da ‘yan matansu, abokai, ko kuma mota da suka mallaka, shi kuwa wannan bawan Allah akuyace yaga tayi mishi ya dauki hoto da ita.
Wasu dai sunyi dariya akan wannan hoton, wasu kuwa haushi abin ya basu.