fbpx
Saturday, June 10
Shadow

Yanda wannan zankadediyar budurwar ta ja ra’ayin wani musulmi ya koma addinin kirista

Wannan budurwar me suna Caramella Mou tayi ikirarin cewa wai ta mayar da wani musulmi kirista, tace mutumin yana tukin motar hayane, suka hadu har ta samu nasarar jan ra’ayinshi yabar addinin shi na musulunci zuwa addinin kiristanci.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ta kara da cewa ya mata alkawarin ranar Lahadi zaije coci kuma zai taimaka a gina cocin.

Ta kuma ce akwai mutane da yawa da suke cikin bata kuma suna bukatar wanda zai iya jajircewa ya gaya musu gaskiya.

A karshe tayi kira ga ‘yan uwanta mabiya addinin kiristanci da su mike tsaye domin aikin da ya kamata ace sunayi kenan (na mayar yiwa mutane wa’azi dan su koma addinin kiristancin).
Tun bayan data wallafa wannan labarai nata a dandalin sada zumunta da muhawara na Twitter, sai labarin nata ya dauki hankalin mutane akayi ta mayar da martani kala-kala. 


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Karanta wannan  Mun nunawa Abba Gida-Gida Soyayya amma ya nuna mana kiyayya>>Inji Wani da aka rushewa shago a Kano

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *