fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Yanda wasu Manya da kananan Sojoji suka bar yaki da Boko Haram suka koma kamun kifi a Borno

Rahotanni sun bayyana cewa akwai sakaci ta bangaren wasu sojoji dake yaki da Boko Haram a Borno.

 

Hakan ya bayyana ne ta bakin wata Majiya daga fadar shugaban kasa, kamar yanda Hutudole ya samo faga The Nation. Majiyar ta bayyana cewa bayan harin da aka kaiwa gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum a hanyarshi ta zuwa Baga.

Gwamnan ya gana da shugaban kasa, Muhammadu Buhari inda suka tattauna kan maganar harin nashi da matakan da ya kamata a dauka dan maganin wannan Ibtila’i.  Majiyar tace alamu sun nuna ba Boko Haram bane suka kaiwa gwamnan Zulum hari ba.

 

Shi kanshi shugaba Buhari ya kadu da jin bayanin abinda ke faruwa na sirri da aka bashi. Dalilin hakane ya yanke shawarar yin garambawul wa Sojojin dake yaki da Boko Haram a Arewa maso Gabas, Hutudole ya samo cewa, Majiyar ta tona Asibirin wasu manyan Sojoji na amfani da Baga suna kamun kifi da noma dan tara Abin Duniya maimakon yaki da Boko Haram.

Karanta wannan  An zargi gwamnatin Zulum da biyan malaman makaranta Albashin Naira Dubu 6

 

Majiyar ta kara da cewa, idan sojojin Najeriya suka dage cikin watanni 6 zasu iya gamawa da Boko Haram. Hutudole ya fahimci cewa an bayyana wani babban soja dake da wata babbar Gona a garin baga.

 

Majiyar ta kara da cewa, Garin Baga ne ke samar da kaso 45 cikin 100 na busashshen kifin da ake ci a Najeriya sannan kuma kasar garin nada Albarkar kayan gona, musamman kayan lambu. Wannan daliline yasa sojojin suke son zama a garin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

1 Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.