A ranar Talatane, 26 ga watan Disamba, kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara yayi murnar zagayowar ranar haihuwarshi, inda ya cika shekaru hamsin a Duniya, Yakubu Dogara yayi amfani da wannan dama ta zagayowar ranar haihuwarhi inda ya tara kudi naira miliyan dari uku, yayi amfani dasu wajan sayawa ‘yan gudun hijira abubuwan bukata.
Yakubu Dogara ya tara wadannan kudinne ta hanyar yin wani littafi akan tarihin rayuwarshi kuma yayi amfani da ranar zagayowar haihuwarshi ya kaddamar dashi, ‘yan majalisar tarayya da manyan jami’an gwamnati da damane suka taru wajan kaddamar da wannan littafi kuma kudin fansar wannan littafinne akayi amfani dasu wajan sayawa ‘yan gudun hijirar kayan tallafi.
Muna mishi fatan Alheri.