Sunday, May 31
Shadow

Yanda ‘yan kasuwar Kantin Kwari, Wambai suka zillewa dokar hana zirga-zirga suka bude sabuwar Kasuwa a Kano

Dokar hana zirga-zirga ta sa an kulle kasuwanni a mafi yawan jihohin Najeriya wanda ba a Najeriya ne kadai lamarin ke faruwa ba dalilin cutar Coronavirus/COVID-19.

 

A jihar Kano ma haka lamarin yake saidai kulle kasuwar yasa wasu da dama na tsitsi ganin cewa kasuwanci na da karfi a cikin Kano.

 

A lokacin da gwamnan jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya sassauta dokar hana zirga-zirga a ranar 2 ga watan Mayu yace an yi hakanne dan baiwa mutane dama su dayi kayan Abinci dan Watan Ramadana.

 

Sanarwar ta kara da cewa kayan Abinci da mayanka kawai za’a sayar sannan dole a saka abin Rufe hanci da baki dan dakile yaduwar cutar da kuma kula da tsafta, sannan a rika nesa-nesa da juna.

 

Saidai ba hakan ke faruwa ba a sabuwar Kasuwar da ‘yan kasuwar Kantin Kwari data Kofar Wambai suka bude a Fage ba.

 

‘Yan kasuwar na cin karensu babu babbaka a cikin unguwar Fage inda gidajen jama’a suke.

 

Kuma mafi yawanci basa amfani da Avin rufe fuska kuma ba’a Nesa-nesa da juna. Wani da yayi hira da Premium times cikin ‘yan kasuwar me suna Nafiu Ubale, ya bayyana cewa dolece ta sashi fitowa dan yana son samarwa iyalanshi abin hidimar Sallah, yace amma suna kokarin kiyayewa dan kada su yada cutar inda yace yana amfani da abin rufe hanci.

 

Shima wani me suna Nura ya bayyana cewa gaskiya bashi da zabine da yawuce ya fito kasuwar shiyasa suka zabi fage saboda itace kusa da kasuwarsu dan su samawa iyalansu abinci.

 

Saidai wani mazaunin Fagen, Abdullahi Kausi wanda ma’aikacin Gwamnati ne ya bayyana cewa ya kamata Gwamnati ta duba ta kawo tsarin da zai hana cutar yaduwa saboda ‘yan kasuwar na sha’aninsu ba tare da nesa-nesa da juna ba sannan kuma basa saka bin rufe hanci da baki.

 

Da aka tuntubi me magana da yawun hukumar ‘yansandan jihar, Abdullahi Haruna ya bayyana cewa suna kokarin ganin ana bin doka inda yace kotun tafi da gidanka da ake amfani da ita wajan hukunta masu karya dokar, ymta hukunta mutane da dama da aka kama suna wa dokar karantsaye.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *