Akwai ‘yan uwa da hadiman shugaban kasa, Muhammadu Buhari 6 da suka nemi takarar kujerun siyasa a bangarori daban-daban amma babu wanda yayi nasara.
Daga ciki akwai Bashir Ahmad.
Bashir Ahmad tsohon hadimin shugaban kasa ne dake bashi shawara kan kafafen sadarwa na zamani.
Ya kuka nemi takarar kujerar dan majalisa a mazabarsa ta Gaya/Aningi/Albasu amma bai nasara ba.
Akwai kuma Sha’aban Sharada wanda tsohon me baiwa shugaban kasa shawara ne kan yada labarai.
Shima ya nemi kujerar gwamna a APC a Kano amma bai sami nasara ba.
Akwai kuma Ismaeel Ahmed wanda tsohon me baiwa shugaban kasar shawara ne kan tallafawa mutane.
Ya fito neman takarar sanata a Kano amma daga baya ya janye saboda saka bakin gwamna Ganduje da neman sulhu.
Akwai kuma Sani Sha’aban wanda suruki ne a wajan shugaban kasa, Muhammadu Buhari inda shima ya fito takarar neman kujerar gwamna a Kaduna amma bai yi nasara ba inda ya kare da kuri’u 20 kacal.
Akwai kuma Fatuhu Muhammad wanda ya nemi sake komawa majalisa wakilatar yankin Daura amma shima ya sha kasa.
Shima dai dan uwane a wajan shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Akwai kuma Faruq Adamu wanda shima wani na kusane ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari wanda ya nemi takarar gwamna a jihar Jigawa amma bai yi nasara ba.