fbpx
Friday, August 12
Shadow

Yankunan Arewa maso gabas dana kudu maso kudu sun fi samun zaman lafiya a mulkina fiye da mulkin da aka yi a baya>>Shugaba Buhari

Me magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya bayyana cewa, yankunan Arewa maso gabas dana kudu maso kudu, sun fi samun zaman lafiya a mulkin shugaba Muhammadu Buhari.

 

Garba ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin din Channels ranar Litinin.

 

Yace duk da ana samun matsaloli nan da can amma maganar gaskiya itace, an samu gagarumar nasara idan aka kwatanta da mulkin baya.

 

Yace a shekarar 2015 da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya hau mulki, Boko Haram na rike da yankin da girmansa ya kai kasar Belgium kuma auna karbar Haraji.

Karanta wannan  Zamu yiwa 'yan bindiga luguden wuta domin shine kadai yaren da suke fahimta basa jin magana, cewar shugaba Buhari

 

Yace amma yanzu basa rike da wadannan gurare, dan haka an yi nasara sosai.

 

Yace matsin da akawa ‘yan Boko Haram a yankin Arewa maso gabas ne yasa suka tsere suka koma yankin Arewa maso yamma.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.