fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Yansanda na binciken kisan da akawa Fulani 2 a jihar Ebonyi

Yansanda a jihar Ebonyi sun yi Allah wadai da kisan da akawa wasu matasan Fulani 2 a Dajin Ishieke dake karamar hukumar Ebonyi a jihar.

 

Wanda aka kashe din sune Adamu Ibrahim dan Shekaru 7 da Jubril Ibrahim da shekaru 15, Rahoton ‘yansanda da kakakin ‘yansandan jihar, Loveth Odah ta fitar ya bayyana cewa an kaiwa fulanin hari rugarsu ne inda aka kashe yaran 2.

Hukumar ‘yansandan tace ta fara binciken lamarin inda kuma ta jawo hankalin mutane da kada a ce za’a je harin daukar fansa a kwantar da hankula.

Leave a Reply

Your email address will not be published.