Wani magidanci me suna Muhammad Tukur dan shekaru 22 ya mutu bayan da suka kachame da Abdullahi Sale shima me shekaru 22.
Premium times ta ruwaito cewa, Tukur ya zargi Sale da yin lalata da matarshi. Lamarin ya farune a kauyen Rabadan dake karamar hukumar Birnin Kudu a jihar.
Kakakin ‘yansandan jihar, Lawan Adam ya bayyana cewa, kwamishinan ‘yansandan jihar ya bada umarnin yin bincike kan lamarin.