fbpx
Saturday, August 20
Shadow

‘Yansanda sun kama magidanci da ya kashe matarsa a jihar Jigawa

‘Yansanda a karamar hukumar Sule Tankarkar dake jihar Jigawa sun kama wani magidanci dan shekaru 26 da ya kashe matarsa me shekaru 23.

 

Kakakin ‘yansandan jihar, Lawal Shiisu ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace Wanda aka kama, Yusuf Zubairu dake zaune a Fulanin Mailefe a kauyen Baldi ya kashe matarsa, Fatima Hardo Dare da sanda.

 

Ya daketa da sandarne bayan da rikici ya barke tsakaninsu, an kira ‘yansanda inda suka garzaya da ita asibiti Likitoci suka tabbatar da ta mutu.

Karanta wannan  Gwamnatin tarayya zata rika biyan tsohon shugaban kungiyar MEND dake satar danyen man Fetur Biliyan 4 duk wata dan ya hana satar danyen man

 

An kama Yusuf da sandar da yayi kisan da ita. Kamar yanda kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN ya ruwaito.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.