An kama wani me suna Nasiru Idris da katukan zabe 101 a jihar Sokoto.
Mutumin ya fito ne daga karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, Hussain Gumel ne ya bayyana haka inda yace sun samu bayanan sirri ne da suka kai ga kama wanda ake zargin.
Ya kara da cewa sun kamashi ne ranar 10 ga watan Oktoba, kuma ya kasa kusu bayanin yanda ya samu katukan.
Yace zasu mayarwa da hukumar zabe me zaman kanta, INEC da katukan.