‘Yansanda sun kashe ‘yan Bindiga da akewa lakabin wadanda ba’a sani ba a jihar Anambra
Ana zargin ‘yan Bindigar masu garkuwa da mutanene kuma an kashesune bayan musayar wutar da aka yi tsakaninsu da jami’an tsaron.
Kakakin ‘yansandan jihar, DSP Toochukwu Ikenga ne ya bayyana haka inda yace lamarin ya farune a daren talatar data gabata.
Yace sun kwace motar ‘yan Bindigar kirar Toyota da kuma Bindigu guda 2.