fbpx
Thursday, July 7
Shadow

‘Yansanda sun kashe ‘yan Bindiga 2 a jihar Katsina

‘Yansandan jihar Katsina sun kashe ‘yan Bindiga 2 a kokarin ganin an kakkabe sauran ‘yan ta’addar da suka yi saura a jihar.

 

Kakakin ‘yansandan jihar, Gambo Isa ne ya tabbatar da haka ga manema labarai inda yace an kashe ‘yan Bindigar ne yayin da suka kai hari a kauyen Kahiyal dake Bugaje, Karamar hukumar Jibia.

 

Yace an kira ‘yansanda yayin da ‘yan Bindigar suka kai hari inda su kuma suka garzaya wajan da lamarin ke faruwa.

 

Yace sun tare hanyar da ‘yan Bindigar zasu bi su tsere inda anan ne aka kashe 2 dsga cikin. Yace an kuma kwato Bindigar AK47.

Leave a Reply

Your email address will not be published.