Shugaban hukumar ‘yansandan Najeriya, Usman Baba ya bayyana cewa sun kai jiragen sintiri da zasu rika aiki tsakanin titin Kaduna zuwa Abuja.
Ya bayyana hakane a Abuja wajan wani taro. Da aka yi kan matsalar tsaro.
Yace an dauki wannan mataki ne dan taimaka ‘yansandan dake fama da ‘yan Bindigar a kasa.
Yace wannan mataki ne da suka dauka na tsaftace hanyar ta Abuja zuwa Kaduna.