Tsohon Mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa, a yanzu da aka janye dakatarwar da akawa Twitter, ‘yan Najeriya zasu shaki iskar ‘yanci.
Atiku ya bayyana hakane a shafinsa na Twitter inda yace dakatar da manhajar da gwamnati tayi, ya taba kananan ‘yan kasuwa.
Yace ‘yan Najeriya da hakan ta taba, yanzu zasu shaki iskar ‘yanci.