fbpx
Thursday, September 29
Shadow

Yanzu da wadannan 3n zasu mutu a inda ba’a sansu ba, wacece zaka ce musulmace?>>Kwamishiniyar Jihar Bauchi ta tambaya

Kwamishiniyar kimiyya da fasaha ta jihar Bauchi, Maryam Garba Begel ta tambaya cewa, tsakanin wadda ta lashe gasar sarauniyar kyau ta Najeriya,  Shatu Garko, da diyar Gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje,  Watau Fatima, da Diyar Sarkin Bichi, surukar shugaban kasa, Zahra waccece idan suka mutu a inda ba’a sansu ba za’a ce musulmace a mata sallah yayin da suke cikim irin wadannan shigar?

Lashe gasar da Garko ta yi ya jawo cece-kuce sosai inda har BBChausa ta yi hira da Hisbah suke cewa, gasar sarauniyar kyau ta sabawa addinin Musulunci.

Karanta wannan  Kasar Qatar ta sassauta haramcin shan giya saboda gasar cin kofin Duniya

 

An samu Rahotannin cewa, HISBAH ta gayyaci iyayen Garko, saidai daga baya hukumar ta karyata wannan rade-radi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published.