fbpx
Tuesday, September 29
Shadow

Yanzu haka mutane 51 ne suka kamu da cutar Numfashi Covid-19 a Najeriya

Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya ta tabbatar da cewa mutanan da suka kamu da cutar coronavirus a kasar sun kai mutane 51.

Hukumar ta NCDC, a shafinta na yanar gizo da kuma shafinta na Twitter, ta bayyana cewa, “Ranar 25 ga Maris, 2020, an sake samun wasu sabbin wandanda suka kamu da cutar Covid-19 har mutum 6.

“Daga cikin sabbin mutum shida da a ka tabbatar a ranar 25 ga Maris, biyu daga jihar Legas, daya a jihar Osun, daya a jihar Ribas, biyu kuma daga Babban birnin tarayya.

A cewar NCDC “Uku sun dawo daga kasashan waje zuwa Najeriya kuma biyu suna da kusanci da wadanda aka tabbatar da lamarin.

A daran Laraba ne da misalin 11:25 na dare, 25th ga watan Maris, aka tabbatar da wandanda suka kamu da cutar Covid19 sun kai kimanin mutum 51 – wanda an sallami mutum biyu, sannan an samu mutuwar mutum guda.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *