fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Yanzu ne lokacin da ya kamata a bada zakka>>Matar Gwamnan Kaduna

Matar gwamnan Kaduna, Hajiya Hadiza Ismail El-Rufai ta jawo hankulan musulmai inda tace wannan lokaci da ake ciki shine mafi dacewar bada zakka.

 

Ta bayyana hakane a shafinta na sada zumunta inda tace itama zata bayar da tata zakkar.

 

Ta bayyana cewa itama zata bayar da zakkarta amma a dunkule zata bayar ga wata kungiya da zata sayi kayan abinci ta rabawa mutane.

Saidai daga baya Ta tambayi shawarar ko ta sayi kayan abinci ta raba ko kuwa ta bayar da tsabar kudi?

Daga baya an bata shawarar bada kudin kamar yanda addini ya tanada, ta kuma amince inda tace zata baiwa na kusa da ita mafiya bukata.

 

Saidai tace zata kuma baiwa sauran mutane sadaka.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.