Dansandan Najeriya, Babatunde Adebayo Me mukamin ASP dake aiki a Legas ya shiga hannu bayan da aka ganshi yana shan Wiwi a bainar jama’a.
Bidiyon Adebayo ya watsu sosai a shafukan sada zumunta inda aka ganshi yana zukar wiwinsa.
Hukumar ‘yansandan jihar ta fitar da sanarwar cewar ta gano dansandan kuma za’a hukuntashi.