Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Ekiti, Oyebanji Filani ya bayyana a yau ranar asabar cewa an samu mutane 74 dauke da cutar Covid-19 a jihar.
Likitan yace dole mutane su cigaba da saka takunkumin fuska da kuma wanke hannaye da sabulu ko kuma sinadarin wanke hannu.
Inda kuma ya kara da cewa ya kamata mutane su cigaba da zuwa ana yi masu rigakafin cutar domin rage yaduwarta da kuma magance cutar baki daya.