fbpx
Friday, July 1
Shadow

Yanzu Yanzu: An zabi gwamna Ganduje don jagorantar tawagar APC a zaben gwamnan jihar Edo

Gwamnan Kano Abudullahi Umar ganduje ne zai jagoranci tawagar APC a zaben Gwamnan Jihar Edo.

Haka zalika shima Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya jaddada cewa ko tantama baya yi cewa jam’iyyar APC ce za ta yi nasara a zabukan gwamnoni dake tafe a kasar nan.

Bello ya bayyana haka ne bayan ganawa da kungiyar kwamitocin yankin Arewa Maso Tsakiya da suka yi da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Ibrahim Gambari.

Inda Manema labarai suka tattauna da shi bayan sun kammala ganawar a fadar shugaban kasa.

A nata bangaran jam’iyyar PDP a jihar Edo kunji cewa gwaman jihar Godwin Obaseki ya canza sheka zuwa jam’iyyar PDP,  inda Gwamnan ya ce ya shiga PDP ne domin “ya samu cimma burina sa na sake lashe zaben gwamnan jihar Edo.”

Karanta wannan  Rochas Okorocha ya roqi babbar kotun tarayya ta bar shi yaje kasar waje neman lafiya kafin ta cigana da sauraron shari'arsa na satar kudin gwamnati

A makon jiya ne kwamitin tantance masu neman takarar gwamna na jam`iyyar APC a jihar Edo ya tabbatar da cire Gwamna Godwin Obaseki daga cikin waɗanda za su yi takarar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.