An gudanar da Sallar Janazah (Jana’izar) na Marigayi Alaafin na Oyo Oba Lamide Adeyemi a kan gawarsa a tsohuwar fadar da ke cikin Garin Oyo.
Babban Limamin Oyoland Sheikh Moshood Ajokidero ne ya jagoranci sallar.
Jana’izar ta samu halartar malaman addinin musulunci da masu jaje da wasu ‘yan siyasa.