Kwamitin John Oyegun da ya tantance ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC me mulki da suka sayi fom akan Naira Miliyan 100 yace guda 10 basu cancanta ba.
Kwamitin yanzu haka ya je ofishin jam’iyyar APC dan mika sakamakon tantancewar da yawa ‘yan takarar.
Saidai Jaridar Vanguard da ta samo labarin tace bata samu sunayen ‘yan takarar ba.