Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa wato ASUU ta janye yajin aikin datake yi na tsawon watanni takwas.
Kungiyar ta janye wannan yajin aikin ne a wani taron gaggawa data gudanar daga daren alhamis zuwa safiyar yau juma’a.
Inda ta bukaci malamai da sauran dalibai bakidaya dasu gaggauta komawa makaranta domin a cigaba da karatu.
ASUU ta janye wannan yajin aikin ne bayan kotun daukaka kara ta tarayya ta umurceta data yi hakan, kuma kungiyar ta kasance tana yajin aiki tun ranar 14 ga watan Febrairu.